Fuad Shukr
Fuad shukr, (Larabci: فؤاد شكر; 15 an haife shi ranar 15 ga watan Afrilu, 1961 - 30 ga watan Yuli 2024; wani lokaci yakan rubuta Fouad Shukar kuma wanda ake yi masa lakabi da Al-Hajj Mohsen ko Mohsen Shukr)[1]ya kasance shugaban mayakan Lebanon wanda babban memba ne na Hezbollah, Shukr babban jigo ne na soja a kungiyar tun farkon shekarun 1980. Sama da shekaru arba'in ya kasance daya daga cikin manyan sojojin kungiyar kuma ya kasance mai baiwa shugabanta Hassan Nasrallah shawara kan harkokin soji. Shukr, a cewar leken asirin Isra'ila, ya kasance jigo wajen mika tsarin jagorancin Iran ga makamai masu linzami na Hezbollah[2]. An yi imanin ya taka rawa a harin bam na barikin Beirut na 1983, [3] wanda ya kashe sojojin Amurka 241, da na Faransa 58, fararen hula shida da maharan biyu. Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Shukr a matsayin wani ɗan ta'adda na musamman da aka zayyana a duniya a cikin 2013. [4] A ranar 30 ga watan Yuli shekarar dubu biyu da ashirin da hudu (2024), an kashe Shukr a wani harin da Isra'ila ta kai a Beirutt saboda zarginsa da kai harin Majdal Shams kwanaki uku da suka gabata, wanda ya kashe yara 12.[5] Tarihin rayuwaAn haifi Shukr a ranar 15 ga Afrilu 1961, A kauyen Al-Nabi Shayth, a gabashin kasar Labanon, wanda kuma shi ne mahaifar shugaban kungiyar Hizbullah, Abbas al-Musawi. Bayan kafuwar kungiyar Hizbullah, kauyen ya zama daya daga cikin sansanonin da ke karkashinta. An yi imanin cewa gidan Shukr da ke Al-Nabi Shayth shi ne na karshe da aka sani da Ron Arad matukin jirgin yakin Isra'ila da ya bace a kasar Labanon a shekarar 1986. Shukr ya yi karatunsa na soja a jami'ar Imam Hossein da ke Tehran.[6] Manazarta
|