Hari a Izghe
Harin Izghe wani lamari ne na ta'addanci da ya faru a ranar 15 ga Fabrairu, 2014.[1] HariWasu ƴan bindiga da ake zargin ƴan ƙungiyar Boko Haram ne sun shiga ƙauyen Izghe da ke jihar Borno da sanyin safiya inda suka kashe maza 105 da tsohuwa 1.[2][3] Yanda harin ya faruWasu gungun mutane sun je wani ƙauye mai suna Izghe da ke jihar Borno, inda suka kashe mutane 106. Ƴan bindigar da ake zargin ƴan ƙungiyar Boko Haram ne. Sun "Kashe sama da mutane 100, ana zargin 'yan Boko Haram ne a harin da ya faru a karamin kauye da ake noma, Izghe, a Borno, Nigeria."[4] Ɗaya daga cikin mutanen da ke da hannu a harin sai da ya tsallake shinge domin ceto rayuwarsa. "Wani wanda ya tsira daga harin ya haura katangar gidansa kuma ya yi ta rarrafe na tsawon mintuna 40 domin tsira."[5] An kai harin ne da yammacin ranar Asabar, 16 ga Fabrairu, 2014. "Mazauna kauyen su ne aka kai wa harin da yammacin ranar Asabar."[4] Inda aka kai harin shine ƙauyen Izghe, wani ƙauye a Najeriya. "Sun bi gida-gida don zaƙulo maza mazaunan da ke ɓoye." [5] Wani hari a KondugaWannan wani ɓangare ne na hare-haren Boko Haram a watan Fabrairun 2014; kisan kiyashin Konduga ya faru a wannan rana shima. Bayan nanBayan ƴan kwanaki, an sake yin kisan kiyashi a ƙauyen.[6][7] ƁarakaAn kai harin ne da nufin sanya al'ummar kasar shiga yaki. "A coci-coci inda ake kai hare-haren bama-bamai, mutane da yawa na ganin an yi yunƙurin haifar da baraka tsakanin Kirista da Musulmi da kuma watakila jefa Najeriya cikin yaƙin basasa wanda ya ɓarke tsakanin ɓangarorin biyu na tsattsauran ra'ayin addini." "[8] Hakan ya faru ne inda maharan suka shiga kauyen suka kashe fararen hula da dama. Manazarta
|