Sojojin Sweden a cikin 'Yantacciyar Jihar Kwango
A tsakanin shekarun 1885 da 1908, sojojin da yawa sun taimaki Sarki Leopold II a mulkin mallakar kasar Kwango a dalilin biyansu mai tsoka da kuma damammaki da zasu samu daga gare shi. Mutanen Sweden zasu zamo na uku a yawan 'yan kasa a cikin sojojin Leopoldo II,[1] kuma a wasu lokutan zasu rika fuskantar kabilun kasar Kwango a yaki. Duk da haka, tare da cewa an mika kasar Kwangon Leopoldo II ga kasar Belgium, da kuma tsananin shirin dakarun soja warwarewar hadinn kan kasar Sweden da kasar Norway, mafi yawan sojoji dole suka koma Sweden.[2] Tushen LabariAna tsananin bukatar kahon giwa da roba a Turai a karshen karni na goma sha takwas, mafi akasari saboda kirkirar tayoyin roba,[3][4] Kasar Kwango na da arzikin wadannan albarkatu hakan ya sa ta zamo kasar nema a Afurka. Bayan Taron Berlin 1884-1885, an amince da yankunan da Leopoldo II yake mulka a shari'ance, duk da cewa yarjejeniyar takarda ce kawai, amma a zahiri kabilun gargajiya da masarutu ke mulkar mafi akasarin yankunan kasar Kwango.[5] Domin neman kara karfafa sarrafa ma'adanai masu yawa na yankin, Leopoldo ya nemi taimakon sojojin 'yan baranda da su taimaka masa wajen mulkin mallakar kasar Kwango.[6] Sojojin kasar Sweden sun burge Leopold II sosai har ta kai ga ya nemesu su shiga cikin sojojinsa da ake kira Force Publique.[7] Da yawa daga cikin sojojin Sweden sun nuna ra'ayi sosai da damar Leopoldo ya basu saboda babu damammaki da isassun kudi a aikin sojan kasar Sweden, sojojin kuma sun duba damar kasar Sweden ta kara yin wani yaki a gaba yayi karanci inda zai sa samun karin girma a aikin yayi wahala. Jerin sanannun sojojin Sweden wadanda suka yi tafiya zuwa Kwango
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.
Manazarta
|